<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>254</hymn_number>
<title>Allahna, Ka Keƃe Ni, Tsarkake Ni Dominka LW254</title>
<lyrics>[V1]
 1) Allahna, ka keƃe ni, tsarkake ni dominka.
 Bari dukan kwanakina in yi ta yabonka.

[V2]
 2) Kebe hannuwana dai, su yi aikin ƙaunarka.
 Bi da ƙafafuna kuwa har su tafi gun aikinka.

[V3]
 3) Bari muryata ta yi waƙar yabon Allahna.
 Bari leƃunana su furta kullum saƙonka.

[V4]
 4) Nufina duk dukiyata sai ta zama dominka.
 Iyawar da ka bayar sai in mayar don aikinka.

[V5]
 5) Na yarda duk nufina naka nufi ya aikata.
 Zuciyata kuwa taka ce, za ta zama kursiyinka.

[V6]
 6 Ya Allah, ga ƙaunata tare da duk dukiyata.
 Ina nan da shiri kuwa kullum domin bautarka,</lyrics>
</song>